Fulani makiyaya a karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano sun roki gwamnatin jiha da ta tallafa musu da abincin dabbobi domin su samu damar kara samar da madara a yankin.
Shugaban makiyayan yankin (Ardo), Ahmadu Sulaiman, ya yi wannan roko ne yayin tattaunawa da ‘yan jarida a kasuwar shanu ta Falgore a ranar Jumma’a.
Sulaiman ya ce fiye da shanu 5,000 suna yawo a yankin karkashinsa, amma suna fama da rashin abincin dabbobi, ciki har da abinci mai gina jiki wanda zai sa su…
>